No front page content has been created yet.

Latest News

Sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Jami'ar Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri sun ce rundunar sojin kasar ta yi
nasarar dakile wani harin ta'addanci da kungiyar Boko Haram
ta shirya kai wa Jami'ar Maiduguri cikin daren jiya Lahadi,
inda aka rika jin karar harbe-harbe a makarantar.
Majiyoyi daga makarantar sun ce an kusan sa'a guda da rabi
ana jiyo karar harbin indiga da ke nuna musayar wuta tsakanin
Sojin da mayakan na Boko Haram, kafin daga bisani al'amura
su daidaita.
Rahotanni sun ce wasu daliban makarantar da ke jarabawa
sun yi kokarin barin makarantar cikin dare domin tsira da

Read More...
Kasashen Najeriya Nijar da Chadi za su hada hannu don inganta noma

Kasashen Najeriya da Nijar da kuma Chadi na wani aikin
hadin kai da zai inganta yanayin noma a tsakanin kasashen
su da kuma farfado da Tafkin Chadi dake cigaba da tsukewa.
Shugaban hukumar ceto yankunan da rairayi ya mamaye dake
Najeriya, Bukar Hassan ya ce tunda matsalar kwararowar
hamada bata san iyakokin kasashe ba, ya zama wajibi ga
wadannan kasashe dake makotaka da juna suyi aiki tare wajen
farfado da harkar noma da shuka itatuwa domin inganta
rayuwar mazauna kusa da tafkin Chadi.

Read More...
Al'ummar Tunisia na zaben sabon shugaban kasa a yau Lahadi

Sama da mutane milyan 7 ne suka cancanci kada kuri’unsu
a zaben shugabancin kasa da ake gudanarwar yau lahadi a
kasar Turnisia, yayin da aka kafa rumfunan zabe sama da
dubu 13 domin bai wa jama'a damar kada kuri'unsu.
Mutane 24 ne ke takara domin maye gurbin shugaba Caid
Essebsi wanda ya rasu a cikin watan yulin da ya gabata.
An tsara bude rumfunan zabe da misalin karfe 8 na safe
kafin a rufe a 6 na yamma domin bai wa jama’a damar
kada kuri’unsu a wannan zabe mai cike da tariki, lura da

Read More...
Mun shirya yi wa Atiku da PDP jina-jina a Kotun Koli – Oshiomhole

Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomole,
ya jaddada cewa APC za ta yi wa PDP da dan
takarar ta, Atiku Abubakar jina-jina a Kotun
Koli.
Majiyar mu ta PREMIUM TIMES HAUSA, ta bada cikakken
labari a ranar Laraba, yadda Buhari ya
kayar da Atiku a Kotun Sauraren Kararrakin
Zaben Shugaban Kasa a karkashin alkalai
biyar.
Jim kadan bayan kammala shari’ar, Atiku ya
ce hukuncin cin fuska ne da rashin adalci,
don haka zai garzaya Kotun Koli.
Yayin da Oshiomhole ya kammala ganawa
da Shugaba Buhari a jiya Laraba, ya

Read More...
Kashi 7.5 ne karin Harajin ‘VAT’, ba 7.2 ba – Gwamnati

Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed,
ta yi karin hasken cewa daga kashi 5℅ bisa
100℅ zuwa 7.5% aka kara kudin Harajin
Kayayyaki, ba zuwa kashi 7.2% ba.
Zainab ta ce amma ba yanzu za a fara aiki
da sabon tsarin biyan harajin ba tukunna,
har sai Majalisar Tarayya ta amince, kuma
ta yi wa Dokar Harajin ‘VAT’ kwaskwarima.
Kakakin Yada Labarai na Minista Zainab,
mai suna Yunus Abdullahi ne ya yi wannan
karin haske a jiya Juma’a, inda ya kara
cewa an bijiro da wannan karin ne biyo
bayan shawarwarin da Majalisar Bada

Read More...
Kudaden kula da tsaron jihohi sun hada Buratai da gwamnoni dambe

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur
Buratai ya ci wa gwamnonin Najeriya
kwala, inda ya kalubalanci halascin
kudaden tsaro jihohin da gwamnatin
tarayya ke dumbuza musu a duk kowane
wata.
Kudaden da aka fi sani da suna ‘security
votes’, Buratai ya ce wasu gwamnoni na
fakewa da sulken kariya daga tuhuma su na
ragargazar kudaden son ran su.
Sai dai kuma Gwamnan Jihar Ekiti, kuma
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya,
Kayode Fayemi, ya bayyana cewa babban
abin da ake bukata dai dangane da

Read More...
Buhari ba shida niyar jefa yan Najeriya cikin kunci

Kwanaki kadan bayan da Gwamnatin tarayya ta sanar da kara
harajin VAT daga kashi 5 zuwa sama da kashi 7 kan
kayayyakin da jama’a ke saye a fadin kasar, shugaban
kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar bashi da aniyar
jefa yan kasar cikin kuncin rayuwa.
Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi tawagar
shugabannin kungiyar kwadago ta TUC, inda yake cewa
gwamnatin zata cigaba da lalubo hanyar saukakawa jama’ar
kasar halin kuntsin da suke ciki.
Shugaban ya jaddada aniyar gwamnatin sa na aiwatar da shirin
karin sabon albashi.

Read More...
Zaben Taraba : APC Ta Sake Yin Nasara A Kotu

Kotun sauraren korafe-korafen zabe dake Abuja ta tabbatarwa da Farfesa Mohammed Sani Yahaya na Jamiyyar APC, halarcin ci gaba da kalubalantar zaben gwamna a Jihar Taraba, wanda Gwamna Darius Ishiyaku na jamiyyar PDP ya lashe.

Read More...
Har yanzu PDP da Atiku na da kwarin gwiwan samun nasara-Jafaru Abbas

Wani lauya kuma masanin kudin tsarin mulkin kasa, Jafaru Abbas, ya ce, matakin da Jam'iyyar PDP da Dan takarar ta na shugaban kasa Alh Atiku Abubakar, suka dauka na daukaka kara zuwa kotun gaba mataki ne da ya dace kuma yake kan doka da hakan zai cigaba da bunkasa damokradiyyar kasar nan kuma ya tabbatar da sahihancin zaben shekara dubu biyu da sha tara da ta gabata.

Ya ce, daman kotun na da damar watsi da karar da aka shigar gabanta. sai dai abun da ake la'akari da shine ingancin dalili da wannan kotu ta dogara a kai.

Read More...
Yadda Buhari ya kayar da Atiku a kotu

A wata gwagwagwar da aka shafe sama yini
guda cur ana karanto bayanan hukuncin
karar zaben shugaban kasa na 2019, Kotun
Daukaka Kara ta bai wa Shugaba
Muhammadu Buhari nasara a kan abokin
takarar sa, Atiku Abubakar na PDP.
Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban
Kasa, ta kori karar da PDP da Atiku
Abubakar suka shigar, inda suka kalubalanci
zaben shugaban kasa da INEC ta bayyana
cewa Buhari na APC ne ya yi nasara.
Alkalai biyar ne suka gudanar da shari’ar, a
karkashin jagorancin Babban Mai Shari’a
Mohammed Garba.

Read More...
Custom Search